(ABNA24.com) Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidy Karmani ya bayyana cewa; Makiya suna zaton cewa za su iya rusa juyin musulunci, sai dai ba su san cewa tsayin dakan al’ummar Iran da jajurcewarsu za su kunyata Amurka ba.
Karmani ya kara da cewa; Lokaci ya yi da duniya za ta dauki Amurka a matsayin Dagutu,kuma shugabanta Donald Trump shi ne babban Dagutun wannan zamanin.
Limamin na Tehran ya yi ishara da ficewar Amurka daga yarjejeniyar kayyade makamai masu linzami masu cin gajeren zango, sannan ya ce; Hakan yana nuni ne da rashin bai wa lamarin muhimmanci da gwmanatin Amurka ta wannan lokacin take yi.
Dangane da takunkumin da Amurka ta kakabawa ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif, limamin na Tehran ya ce; hakan yana nuna kardar da Amurkan take yi na cewa tana son tattaunawa da Iran.
/129
Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidy Karmani ya bayyana cewa; Makiya suna zaton cewa za su iya rusa juyin musulunci, sai dai ba su san cewa tsayin dakan al’ummar Iran da jajurcewarsu za su kunyata Amurka ba.